8 Faburairu 2016 - 14:26
Naira: Sarki Sanusi ya soki Buhari

Tsohon shugaban babban bankin Nigeria kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta kawo karshen manufofinta na daidaita darajar naira.

Jaridar Financial Time ta ambato Sarkin na cewa "Rashin alherin hakan ya zarta alherin da cikinta."

Hakan ya zo ne bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC cewa har yanzu ba samu wani dalili ba da zai gamsar da shi ya rage darajar kudin kasar.

Faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya dai ya shafi tattalin arzikin kasar.

A hukumance a kasar ana sayar da dalar daya a kan kusan naira 200, sai dai dalar ta kai naira 300 a kasuwar bayan fage.

"Gwamnati ba ta da isassun kudaden ajiya wadanda za su bar darajar Naira ta ci gaba da kasance yadda ake so a hukumance," In ji Sarki Sanusi.

Sarkin ya ce manufar "ba ta taba aiki ba" a duk inda aka gwada.288